إعدادات العرض
Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira
Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira
Daga Abu Salama Ibnu Abdurrahman cewa Jabir Ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su - ya ce: Alhali shi yana bada labari game da lokacin wahayi, a cikin zancensa sai ya ce: "Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira a zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, ai na ji tsoronsa, sai na dawo sai na ce: Ki lulluɓeni, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da {Ya kai mai lulluɓa1 Ka tashi ka yi gargaɗi}[alMuddasir: 2] zuwa faɗinSa: {Ka ƙauracewa gumaka} [al-Muddassir: 5]. Sai wahayi ya tsananta kuma ya bibiyi juna.
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული Kurdî বাংলা ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahili ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતીالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.فوائد الحديث
Yankewar wahayi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan saukar faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Ka yi karatu}.
Halaccin mutum ya bada labarin abin da ya faru gare shi na jarawaba bayan gushewar jarabawar, dan godiya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Farkon abin da ya sauka shine faɗinSa: {Yakai mai lulluɓa} bayan saukar: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta}.
Falalar Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda ya zuba wahayinSa ba tare da yankewa ba har sai da yabar duniya.
Wajabcin tsayuwa da kira zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da yi wa waɗanda suka bijire gargaɗi da yi wa masu biyayya albishir.
Wajabcin tsarkake tufafi dan yin sallah, haƙiƙa sun kafa hujja da faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Ka tsarkake tufafinka}.
Wajabcin yin imani da mala'iku da kuma abin da Allah Ya basu iko a kansa na ayyuka da wasunsu.
