إعدادات العرض
Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka
Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga wurin Ubangijinsa - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, Ya ce: «Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka, wanda ya yi niyyar (aikata) kyakkyawa bai aikatata ba; Allah zai rubuta masa kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan ya yi niyyar yinta sai ya aikatata; Allah zai rubutata a wurinSa kyakkyawa goma har zuwa ninki ɗari bakwai har zuwa ninkin ba ninkin. Idan kuma ya yi niyyar mummuna bai aikatata ba; Allah zai rubuta ta kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan kuma ya yi niyyarta sai ya aikatata; Allah zai rubutata mummuna ɗaya».
الترجمة
العربية Español አማርኛ English اردو Indonesia বাংলা Français Türkçe Русский Bosanski සිංහල हिन्दी 中文 فارسی Tiếng Việt Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ ไทย Deutsch پښتو অসমীয়া Shqip Nederlands ગુજરાતી Кыргызча नेपाली Lietuvių دری Српски тоҷикӣ Kinyarwanda Magyar Čeština Moore Malagasy Oromoo ಕನ್ನಡ Wolof Azərbaycan O‘zbek Українська ქართული Македонски ភាសាខ្មែរ Bambara ਪੰਜਾਬੀ मराठी Kirundi Kurmancî Bahasa Melayuالشرح
Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.فوائد الحديث
Bayanin falalar Allah mai girma ga wannan al'ummar wajen ninka kyawawa da kuma rubutasu a wurinsa, da rashin ninka munana.
Muhimmancin niyya a cikin ayyuka da kuma tasirinta.
Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da saukinsa da kyutatawarsa cewa wanda ya yi nufin kyakkywa bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubutashi a matsayin kykkyawa.
