Ku rage gashin baki, ku cika gemu

Ku rage gashin baki, ku cika gemu

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku rage gashin baki, ku cika gemu".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni da rage gashin baki, kuma kada a barshi, kawai a rageshi, kuma a kai matuƙa a hakan. A ɗaya ɓangaren kuma yana umarni da cika gemu da kuma barinsa a cike.

فوائد الحديث

Haramcin aske gemu.

التصنيفات

Sunnonin Fixra