Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.

[Hasan ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyar da sahabbansa Alƙur'ani yana karantar da su shi a dukkanin halayensa muddin dai bai kasance yana da janaba ta hanyar jima'i ba.

فوائد الحديث

Rashin halaccin karatun Alƙur'ani ga mai janaba har sai ya yi wanka.

Koyarwa a aikace.

التصنيفات

Hukunce Hukunce Al-qur’ani, Ladaban Karanta Al-qur’ani da kuma Haddace shi, Wanka