Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah

Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah

Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah»

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.

فوائد الحديث

An so yi wa wanda mutuwa ta halarto masa talƙini.

An karhanta yawaita yin talƙini ga wanda mutuwa ta halarto masa, da kuma nacewa a kansa idan ya karɓi talƙinin, ko an fahimci hakan daga gare shi; dan kada ya takura masa sai ya furta abin da bai dace ba.

Nawawi ya ce: Idan ya faɗeta sau ɗaya to kada ya maimaita masa saidai idan ya yi wata maganar daban a bayansa, sai asake bijiro masa da ita dan ta zama ita ce ƙarshen zancensa.

Hadisin ya ƙunshi halartar wurin da wanda mutuwa ta halarto masa dan tinatar da shi da kuma yi debe masa kewa da rintse idanuwansa da kuma tsayuwa da haƙƙoƙinsa.

Rashin halaccin yin talƙini bayan mutuwa da wurin ƙabari bayan an binne; saboda rashin aikata hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Mutuwa da Hukunce Hukuncenta