إعدادات العرض
Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne
Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne, a Riwayar Muslim kuma : Matashin kai na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda yake dogara a kan shi ya kasance na jemammiyar fata ne, cikinta kaba ce.
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahili ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતીالشرح
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa shimfiɗar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake kwanciya a kanta ta kasance an yi ta ne da jemammiyar fata, kuma a cike ta ke da kaba ta dabino, haka ma matashinsa wanda yake kishingiɗa a kansa.فوائد الحديث
Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na zuhudu da bijirewa jin daɗin duniya, tare da cewa Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - Ya tabbatar masa da hakan inda a ce ya so ya ji daɗin da ita.
Halaccin mallakar shimfiɗa da matashi, da kuma bacci a kansu dan jin sauƙaƙa yin bacci.
Yana kamata ga musulmi ya lura da halinsa da kuma rayuwarsa da halin Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shine abin koyi mai kyau, kuma wanda ya bi tafarkinsa ya shiriya kuma ya rabauta a duniya da lahira.
Kwaɗayi akan yin tanadi domin lahira, kuma mumini ya wadatu da abin da zai taimake shi akan biyayya ga Allah a duniya, kuma kada ya shagalta da neman tara dukiya a duniya, haƙiƙa Allah Ya zargi wasu mutane sai ya ce: {Alfahari (da yawan 'ya'ya da dukiya) ya shagaltar da ku. Har (kuka mutu) kuka ziyarci ƙaburbura} [al-Takasur: 1-2].
