إعدادات العرض
Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?
Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?
Daga Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული Kurdî বাংলা ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahili ភាសាខ្មែរ English ગુજરાતીالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.فوائد الحديث
Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta hanyar tambayar sahabbai da kuma sasu shauƙin sanin amsa.
Ɗaibi ya ce: Kwaɗaitarwa a kan sulhunta masu rigima da nisantar ɓata su; domin yin sulhu sababi ne na yin riƙo da igiyar Allah da kuma rashin rabuwa tsakanin musulmai, ɓacin masu rigima rabuwa ne a cikin Addini duk wanda ya yi sulhu ya kuma ɗauke ɓacinta zai samu daraja sama da abin da mai azimi mai tsayuwar dare mai shagalta da keɓantuwar kansa yake samu.
