Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu

Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan watan Ramadan ya shiga sai al'amura uku su faru: Na farko: Za'a buɗe ƙofofin aljanna ba za'a kulle wata ƙofa ba daga cikinsu. Na biyu: Za'a kulle ƙofofin wuta, kuma ba za'a buɗe wata ƙofa daga cikinsu ba. Na uku: Za'a ɗaure shaiɗanu da aljanu masu tsaurin kai da sarƙoƙi, ba zasu kai zuwa ga abinda suke tsira da shi a cikin wanin (watan) Ramadan ba. Dukkanin wannan dan girmamawa ne ga wannan watan, da kwaɗaitar da masu aiki akan yawaita ayyukan ɗa'a na sallah da sadaka da zikiri da karatun Alkur'ani da wanin haka; da kuma nisantar zunubai da saɓo.

فوائد الحديث

Falalar watan Ramadan.

Yi wa masu azimi albishir a cikinsa da cewa wannan watan mai albarka mausimi ne na ibada da alheri.

A cikin ɗaure shaiɗanu a cikin Ramadan akwai nuni zuwa ɗauke uzurin mukallafi, kamar cewa shi ana ce masa ne: Haƙiƙa an ɗaure shaiɗanu daga gareka dan haka kada ka bada uzuri da su a cikin barin aikin ɗa'a ko a cikin aikata saɓo,

AlKurɗubi ya ce: Idan an ce: Yaya muke ganin sharruka da saɓo masu yawa suna faruwa a cikin (watan) Ramadan ?da a ce an ɗaure shaiɗanu da hakan bai faru ba? To amsa (ita ce ace): Cewa su (sharruka) suna ƙaranta ne daga masu azimi azimin da aka kiyaye sharuɗɗansa kuma aka lura da ladubbansa, ko kuma waɗanda ake ɗaurewa wasu daga cikin shaiɗanu ne kawai sune masu tsaurin kai ba dukkansu ba kamar yadda ya gabata a cikin wasu daga ruwayoyi, ko kuma abin nufi ƙaranta sharrukansu a cikinsa, to wannan wani al'amari ne abin gani, domin cewa afkuwar hakan a cikinsa shi ne mafi ƙaranci daga waninsa, dan ba ya lazimta daga daure gabadayansu cewa sharri ko sabo ba zai faru ba; domin akwai sabubba ga hakan banda shaidanu kamar munanan rayuka da al'adu munana da kuma shaidanun mutane.

التصنيفات

Falalar Azumi