Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai

Daga Bara’u ɗan Azib -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai: Ya umarcemu da duba mara lafiya, da raka jana’iza, da gaida mai atishawa, da kuma kuɓutar da rantsuwa, ko mai rantsuwa, da taimakon wanda aka zalunta, da kuma amsawa mai gayyata, da yaɗa sallama. Ya kuma hana mu yin zobe - ko sanya zoben zinare, da sha acikin abin sha na azurfa, da al-Mayathir, (Shi ne matakalar abunda ake sanyawa a shinfidar doki) da al-ƙissi (zabon Masar, nau’i ne na alhariri mai kauri) da kuma sanya alharini, da al-Istabraƙ (Alharini mai kauri) Dibaj (shi ma nau’i ne na alharini mai kauri).

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmai da ɗabi'u bakwai kuma ya hanesu ɗabi'u bakwai; waɗanda ya umarce su sune: Na farkonsu: Ziyarar mara lafiya. Na biyunsu: Raka jana'iza da tarayya ta hanyar yi mata sallah da kuma binneta, da yi mata addu'a. Na ukunsu: Yin addu'a ga wanda ya yi atishawa kuma ya godewa Allah, shi ne ace masa: Allah Ya yi maka rahama. Na huɗunsu: Kuɓutar da mai rantsuwa da kuma gasgata shi, ma'ana cewa da zai yi rantsuwa akan wani al'amari alhali kai kana da iko akan sanya shi kuɓutacce a cikinta to ka aikata; dan kada ka bar shi zuwa yin kaffara ta rantsuwar. Na biyarɗinsu: Taimakon wanda aka zalinta, ta hanyar taimaka masa da tunkuɗe abinda yake afka masa daga azzalimi gwargwadan iko. Na shidansu: Amsa gayyata zuwa walimar abin ci, kamar walimar angwanci, ko suna, ko waninsu. Na bakwansu: Yin sallama da yaɗata da kuma amsata. Waɗanda kuma ya hanasu su ne: Na farkonsu: Sanya zobunan zinare da kuma yin ado da su. Na biyunsu: Shan abu a ƙwaryar azirfa. Na ukunsu: Zama akan Mayasir, sune shimfiɗun da ake sawa akan sirdin doki da kuma sirdin raƙumi na alharaini. Na huɗunsu: Sanya tufafin da aka yi da kattanin da aka cakuɗa da alharini kuma ana ambatansa: (Alƙisiyyu). Na biyarɗinsu: Sanya alharaini. Na shidansu: Sanya Istabraƙ, shi ne: Alharini mai kauri. Na bakwansu: Sanya Dibaj, shi ne: Mafi kyan nau'ikan alharini kuma mafi tsadarsu.

فوائد الحديث

Bayanin wani daga cikin haƙƙoƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi.

Asali shi ne dukkan abinda yake zuwa a cikin shari'a na umani ko hani yana game maza da mata, sai dai abinda aka keɓance cewa shi yana daga cikin abinda maza suka keɓanta da shi ko abinda mata suka keɓanta da shi ne.

Wasu Hadisan daban sun yi nuni akan hana mace bin jana'iza.

Wasu Hadisan daban sun yi nuni akan halaccin sanya zinare da alharini ga mace.

التصنيفات

Ladaban Shari'a, Xaukar Mamaci da binneshi