إعدادات العرض
1- Shin ba ku sani ba cewa Musulunci ya shafe abin da yake gabaninsa, hijira kuma ya shafe abin da yake gabaninsa, kuma Hajji ya shafe abin da yake gabaninsa?
2- Duk wanda ya halarci gawa har akai mata salla yana da kiradi guda,wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu,aka ce:menene kiradi biyu?yace:kwatankwacin manyan Duwatsu biyu
3- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai*: Ya umarcemu da duba mara lafiya, da raka jana’iza, da gaida mai atishawa, da kuma kuɓutar da rantsuwa, ko mai rantsuwa, da taimakon wanda aka zalunta, da kuma amsawa mai gayyata, da yaɗa sallama. Ya kuma hana mu yin zobe - ko sanya zoben zinare, da sha acikin abin sha na azurfa, da al-Mayathir, (Shi ne matakalar abunda ake sanyawa a shinfidar doki) da al-ƙissi (zabon Masar, nau’i ne na alhariri mai kauri) da kuma sanya alharini, da al-Istabraƙ (Alharini mai kauri) Dibaj (shi ma nau’i ne na alharini mai kauri).
4- "Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".