Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci…

Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci a tsakaninsu, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da ta aikata, sai ya ce: @«‌Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi».

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci a tsakaninsu, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da ta aikata, sai ya ce: «‌Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa wata mata miskiniya tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu sai ta tambayeta, sai ta bata dabinai uku, sai ta bawa kowacce daga cikin 'ya'yan nata mata biyu dabino ɗaya, kuma ta ɗaga ɗayan zuwa bakinta dan ta ci shi, sai 'ya'yan nata mata biyu suka nemi dabinon da take nufin cinsa, sai ta raba dabinon a tsakaninsu, sai lamarinta ya ƙayatar da Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, kuma ta faɗawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abinda matar ta aikata, sai ya ce: Lallai haƙiƙa Allah Ya tabbatar mata aljanna saboda wannan dabinon, ko kuma ya 'yantata daga wuta.

فوائد الحديث

Falalar sadaka ko da ta kasance kaɗan ce, kuma ita tana nuni akan gaskiyar mumini a cikin imaninsa da Ubangijinsa da kuma amincewarsa ga alƙawarinsa da kuma falalarsa.

Tsananin jin ƙan iyaye mata ga 'ya'yansu da kuma jin tsoron tozarci garesu.

Falalar fifita wani akan kai, da kuma jin ƙan yara ƙana, da ƙarin kyautatawa da kuma rangwami ga 'ya'ya mata, kuma cewa hakan sababi ne na shiga aljanna da kuma 'yantuwa daga wuta.

Kaɗan ba ya hana a yi sadaka da shi saboda ƙanƙantarsa, kai yana kamata ga mai yin sadaka ya yi sadaka da abinda ya sawwaƙa gare shi ya ƙaranta ne ko yana da yawa.

A cikinsa akwai bayanin abinda ɗakunan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suke akai kuma ya rayuwarsa take tare da iyalansa alhali a cikin gidansu babu abinda za'a ci inba dabino ba ko dabinai uku.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai