Na roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya bani, sannan na sake rokonsa sai ya bani, sannan ya ce da ni: @«Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi*, wanda ya karɓeta da wadatar rai, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da ɗaukakar rai…

Na roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya bani, sannan na sake rokonsa sai ya bani, sannan ya ce da ni: @«Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi*, wanda ya karɓeta da wadatar rai, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da ɗaukakar rai ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, sai ya zama kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki shi ne mafi alheri daga hannu maƙasƙanci». Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan taɓa tauye wa wani, wani abu ba a bayanka har na bar duniya, Abubakar ya kasance yana kiran Hakim dan ya bashi kyauta (daga Baitul mali), sai ya ƙi karɓar komai daga gurinsa, sannan Umar ya kira shi dan ya ba shi, sai ya ƙi karɓa, sai ya ce: Yaku jama'a musulmai, lallai cewa ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga wannan ganimar, sai ya ƙi karɓarsa, Hakim bai tauyewa wani mutum daga cikin mutane ba bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - har sai da ya rasu - Allah ya yi masa rahama -.

Daga Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce:: Na roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya bani, sannan na sake rokonsa sai ya bani, sannan ya ce da ni: «Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi, wanda ya karɓeta da wadatar rai, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da ɗaukakar rai ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, sai ya zama kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki shi ne mafi alheri daga hannu maƙasƙanci». Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan taɓa tauye wa wani, wani abu ba a bayanka har na bar duniya, Abubakar ya kasance yana kiran Hakim dan ya bashi kyauta (daga Baitul mali), sai ya ƙi karɓar komai daga gurinsa, sannan Umar ya kira shi dan ya ba shi, sai ya ƙi karɓa, sai ya ce: Yaku jama'a musulmai, lallai cewa ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga wannan ganimar, sai ya ƙi karɓarsa, Hakim bai tauyewa wani mutum daga cikin mutane ba bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - har sai da ya rasu - Allah ya yi masa rahama -.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wani abu na jin daɗin duniya sai ya ba shi, sannan ya roke shi karo na biyu sai ya ba shi, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Ya Hakim, lallai cewa wannan dukiyar abar sha'awace abar so ce, wanda ya sameta ba tare da roƙo ba kuma ya karɓeta ba tare da zari da kuma naci ba, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da tsinkayar rai da kuma kwaɗayi ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, zai zama kamar wanda yake ci ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki mai bayarwa shi ne mafi alheri a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo. Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya ba zan karbi dukiyar wani ba ta hanyar roko daga gare shi ba a bayanka har na bar duniya. Halifan Manzon Allah Abubakar - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana kiran Hakim dan ya ba shi rabonsa daga baitul mali, sai ya ƙi karɓar komai daga gare shi, sannan sarkin muminai - Umar - Allah Ya yarda da shi - ya kira shi dan ya ba shi ita, sai ya ƙi karɓarta, sai Umar ya ce: Yaku taron jama'ar musulmai, lallai ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga ganimar da musulmai suka samu daga kafirai ba tare da ya ƙi ba, sai ya ƙi karɓarta, bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Hakim bai rage dukiyar kowa ba ta hanyar nemanta har ya yi wafati - Allah Ya yarda da shi -.

فوائد الحديث

Karɓar dukiya da tarata ta hanyar da aka shara'anta ba ya cin karo da gudun duniya; domin gudun duniya wadatuwar zuciya ne da kuma rashin rataya zuciya da dukiya.

Bayanin girman karamcin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa shi yana bada kyautar wanda ba ya jin tsoron talauci har abada.

Yin nasiha da kuma kwaɗayi akan amfanar da 'yan uwa a lokacin neman taimako; domin zuciya tana kasancewa mai shirin karɓar amfani ta hanyar zantuttuka masu daɗi.

Kamewa daga roƙon mutane da kuma kore shi musamman ma dai in babu wata buƙata.

A cikinsa akwai zargin kwaɗayi akan dukiya da kuma yawan roƙo.

Mai roƙo idan ya nace akan roƙon, to babu laifi idan an ƙi ba shi, da taɓar da shi da kuma yi masa wa'azi, da umartarsa da kamewa da kuma barin kwaɗayi akan karɓa.

Ba wanda ya cancanci karɓar wani abu daga baitul mali sai bayan shugaba ya ba shi shi, amma kafin raba ganima to hakan ba haƙƙinsa ba ne.

Halaccin roƙo saboda buƙata.

Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa yana kamata ga shugaba kada ya bayyanawa mai roko abinda ke cikin roƙonsa na ɓarna sai bayan ya biya masa buƙatarsa, dan wa'azinsa ya dace da gurbinsa, dan kada ya riya cewa hakan wani sababi ne na hana shi buƙatarsa.

A cikinsa akwai falalar Hakim - Allah Ya yarda da shi - da kuma dorawa kansa alƙawarin da ya yi tare da Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Ishaƙ ɗan Rahuwaih ya ce: Hakim - Allah Ya yarda da shi - ya rasu, a lokacin da ya rasu yana daga cikin mafiya yawan Ƙuraishwa a dukiya.

التصنيفات

Zargin Son Duniya