«Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa*, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita,…

«Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa*, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita, sai suka sha suka shayar, kuma suka yi shuka, kuma ruwan ya samu wani ɓangare daban, wanda shi kawai faƙo ne ba ya riƙe ruwan kuma ba ya tsirar da ciyawa, to hakan kwatankwacin wanda ya fahimci Addinin Allah ne kuma Ya amfanar da shi da abinda Allah Ya aikoni da shi, sai ya sani ya kuma sanar, da kwatankwacin wanda bai ɗaga kai ba da hakan, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wacce aka aikoni da ita ba».

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita, sai suka sha suka shayar, kuma suka yi shuka, kuma ruwan ya samu wani ɓangare daban, wanda shi kawai faƙo ne ba ya riƙe ruwan kuma ba ya tsirar da ciyawa, to hakan kwatankwacin wanda ya fahimci Addinin Allah ne kuma Ya amfanar da shi da abinda Allah Ya aikoni da shi, sai ya sani ya kuma sanar, da kwatankwacin wanda bai ɗaga kai ba da hakan, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wacce aka aikoni da ita ba».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta yana mai ban ammaki wanda yake anfanuwa da abinda ya zo da shi na hujjoji da kuma hanyar da zata kai zuwa ga abin da ake nema, da kuma ilimi na shari'a da ƙasar da ruwa mai yawa yake sauka a ita; sai ta zama ta kasu kaso uku: Na farkonsu: Tsarkakakkiyar ƙasa mai tsarki, wacce take karɓar ruwan sama, sai ta tsirar da tsirrai mai yawa ɗanye da busasshe, sai mutane suka amfana da ita. Na biyunsu: Ƙasar da take riƙe ruwa, saidai ba ta tsirar da shuka, ita tana kiyaye ruwa dan mutane su amfana da shi; sai su sha su shayar da dabbobinsu da kuma shukarsu. Na ukunsu: Ƙasa madaidaiciya mai santsi wacce ba ta riƙe ruwa kuma ba ta tsirar da shuka, ita akan kanta ba ta amfana da ruwan da hakan ba, haka kuma mutane basu amfana da ruwan ba. Haka nan masu jin abinda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na ilimi da kuma shiriya. Na farko: Malami wanda ya fahimci Addinin Allah, mai aiki da iliminsa, mai sanar da waninsa; shi a matsayin ƙasa ce mai tsarki wacce ta sha ruwa sai ta amfana ita akan kanta, kuma ta tsirar sai ta amfani waninta. Na biyu: Mai haddace ilmi sai dai ba shi da fahimta da kuma istinbaɗi, shi ya tara ilimi, ya dilmiyar da lokacinsa a cikin hakan, sai dai cewa shi bai yi aiki da nafilfilinsa ba, ko bai fahimci abinda ya tara ba; to shi ala ce ga waninsa, kuma a matsayin ƙasa ce wacce ruwa ba ya tabbata a cikinta ballantana mutane su amfana da shi. Na uku: Wanda yake jin ilimi ba ya haddace shi, ba kuma ya aiki da shi, kuma ba ya ciratarsa ga waninsa; to shi a matsayin ƙasar gishiri ce ko ƙasa mai santsi wacce babu tsirrai a cikinta kuma ba ta karɓar ruwa ko tana ɓata shi ga waninta.

فوائد الحديث

Bayanin falalar neman ilimi da sanar da shi, da gargaɗarwa daga bijira daga garesu.

Buga misalai dan kusanto da ma'anoni ga mutane.

AlƘurɗubi ya ce: Kamar yadda cewa girgije yana raya mataccen gari haka nan ilimummukan Addini suna raya matacciyar zuciya, sannan ya kamanta masu jinsa da ƙasa mai banbancin abinda girgijen yake saukar wa na ruwa a kanta.

Mutane matakai ne a karɓar ilimin shari'a.

التصنيفات

Falalar Ilimi