ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya

ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya

Daga Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni: "ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya roƙi Allah ya tambaye shi sai ya ce: (Ya Allah Ka shiryar da ni) Ka shiryar da ni Ka nuna mini (Ka datar da ni) Ka yi mini gam da katar, Ka sanya ni madaidaici a dukkan al'amurana. Shiriya: Ita ce sanin gaskiya a fayyace kuma a dunƙule, da dacewa ga binta a zahiri da baɗini. Dacewa kuwa: Ita ce dacewa da daidaita a dukkanin al'amura da abinda zai zama daidai akan gaskiya, shi ne hanya madaidaiciya a magana da aiki da ƙudiri. Kuma cewa umarni na ma'ana yana bayyana da abin ji; ka tina alhali kai kana yin wannan addu'ar cewa: (Shiriya: Shiriyarka (irin ta) hanya) ka halarto zuciyarka alhali kai kana roƙon shiriya kamar shiriyar wanda ya yi tafiya, cewa shi baya kaucewa akan hanya dama da hagu; hakan dan ya kuɓuta daga ɓata (makuwa), da haka ne zai samu kuɓuta, ya kai zuwa manufarsa a gaggauce. (Daidaita: (irin) daidaitar kibiya) kai kana lura a lokacin da kake daidaita kibiya a gaggawar saduwarta da samunta ga inda aka harbata, mai harbi idan ya harbi inda yake so sai ya daidaita kibiya wajen inda zai harba, to haka nan zaka roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - cewa abinda ka yi niyyarsa na daidai yana kan yanayin kibiya; sai ka zama a roƙonka mai neman matuƙar shiriya, da ƙarshen daidaita. Ka halarto wannan ma'anar a zuciyarka har sai ka roƙi Allah daidai dan abinda ka yi niyyarsa daga hakan ya zama akan yanayin abinda kake anfani da shi na harbi.

فوائد الحديث

Mai addu'a ya kamata ya yi kwaɗayi akan daidaita aikinsa da daidaita shi ta hanyar lazimtar sunna da tsarkake niyya.

An so yin addu'a da waɗannan kalmomin mai tattarowa ga dacewa da daidaita.

Ya kamata ga bawa ya nemi taimakon Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan al'amuransa.

Buga misali a lokacin koyarwa.

Haɗawa tsakanin neman shiriya da gyaruwar hali, da tafiya akansa da rashin karkata daga gare shi koda ƙiftawar ido da gyaruwar makoma, faɗinsa: "Ka shiryar da ni" shi ne ya zama mai tafiya akan hanyar shiriya, da faɗinsa: "Ka datar da ni": Na dacewa da rashin karkacewa a lokacin shiriyar da ya riƙeta.

Mai Addu'a ya kamata gare shi ya himmantu da addu'arsa, ya halarto ma'anonin addu'arsa a cikin zuciyarsa; to wannan ya fi kusa ga karɓuwa.

التصنيفات

Addu’o’I da aka samu daga Annabi