Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: @Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.

Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: @Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.

Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin gidansa kuma me yake aikatawa? Sai ta ce: Ya kasance mutum ne daga cikin mutane, yana aikata abinda maza suke aikatawa a cikin gidajensu, sai ya kasance a cikin hidimar kansa da iyalansa; yana tatsar nonon akuyarsa, yana ɗinke tufafinsa, yana gyara takalminsa, yana ɗinke gugansa, kuma ya kasance idan lokacin tada sallah ya yi sai ya fita zuwa gareta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba tare da wani jinkiri ba.

فوائد الحديث

Cikar tawali'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kyakkyawan mu'amalarsa ga iyalansa.

Ayyukan duniya yana kamata kada su shagaltar da bawa daga sallah.

Kiyayewar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan sallah a cikin farkon lokutanta.

Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan tawali'u da barin girman kai da kuma hidimar iyalai ga namiji.

التصنيفات

Matansa SAW da halin gidan Annabta, Dangantaka tsankanin Mace da Namiji