Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi

Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi

Daga Jundub Ibnu Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.

فوائد الحديث

Bayanin cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.

Jeranta abin da ya fi kamata a lokacin tarbiyyar mai tasowa, da kuma kwaɗayi akan cika musu imani.

Alƙur'ani yana ƙara imani, kuma zuciya tana haskaka da shi, kuma ƙirji yana buɗewa da shi.

التصنيفات

Ladaban Karanta Al-qur’ani da kuma Haddace shi, Qaruwar Imani da Raguwarsa