An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi

An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi

Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce mini: «An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Uƙbah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: A daren nan Allah Ya saukar min da wasu ayoyi ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba - wato a neman tsari (Dafa'i) - sune A'uzai guda biyu: Surar {Ƙul A'uzau bi rabbil falaƙ}, da surar {Ƙul A'uzu bi rabbin Nas}.

فوائد الحديث

Bayanin girman falalar waɗannan surori biyun.

Kwaɗaitarwa akan neman tsari da su daga dukkan sharruka.

التصنيفات

Falalar Surori da Ayoyi