Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne

Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne

Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne».

[Ingantacce ne] [رواه أبو داود والنسائي]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci mazaje masu yin sallah a jam'i da cika sawun farko, sannan da cika sawun da ke biye da shi, idan za’a samu wata tawaya a cikin wani sawu to wannan tawayar ta zama a sawun ƙarshe ne.

فوائد الحديث

Bayanin sunna a kan daidaita sawu.

Ya wajaba akan masallata kada su bar tawaya a cikin sawun gaba, kai tawaya ta zama a cikin sawun ƙarshe ne.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta