إعدادات العرض
Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike
Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike
Daga Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
[Ingantacce ne] [Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shi]
الترجمة
العربية Español አማርኛ English اردو Indonesia বাংলা Français Türkçe Русский Bosanski සිංහල हिन्दी 中文 فارسی Tiếng Việt Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ ไทย Deutsch پښتو অসমীয়া Shqip Nederlands ગુજરાતી Кыргызча नेपाली Lietuvių دری Српски тоҷикӣ Kinyarwanda Magyar Čeština Moore Malagasy Oromoo ಕನ್ನಡ Wolof Azərbaycan O‘zbek Українська ქართული Македонски ភាសាខ្មែរ Bambara ਪੰਜਾਬੀ मराठी Kirundi Kurmancî Bahasa Melayuالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.فوائد الحديث
Falalar dogaro ga Allah, kuma yana daga mafi girman sabubban da ake jawo arziki da su.
Tawakkali ba ya kore sabubba, domin ya ba da labarin cewa tawakkali na haƙiƙa jijjifi da yammaci a neman arziki ba ya kishiyantarsa.
Himmatuwar shari'a da ayyukan zuciya; domin dogaro aiki ne na zuciya.
Rataya da sabubba kawai tawaya ne a addini, barin sabubba kuma tawaya ne a hankali.
