إعدادات العرض
1- Duk wanda ya Yanta wani Rai Musulmi to Allah zai Yanta da kowace Gaba daga jikinsa daga Wuta, har Al-aurarsa da Al-aurarsa
2- Duk wanda ya 'yanda rabonsa na Bawan da sukai tarayya a cikinsa kuma yana da kuxin da zai iya cika ragowar kuxin sai a lissafa masa sauran rabon sauran ya biya don bawan ya 'yantu
3- Duk wanda ya 'yanta rabonsa na wani bawa to ya wajaba akansa ya cika sauran a cikin kuxinsa, idan bashi da shi sai ayi kimar bawan yayi aikin fansa
4- Mutane Uku suna da Lada biyu: wani Mutum daga cikin Ahlul-Kitab da yayi Imani da Annabinsa, kuma yayi Imani da Annabi Muhammad, da kuma Bawan da ya bada Hakkin Allah da Hakkin Mai gidansa, da Kuma Mutumin da ya ke da baiwa ya kyautata tarbiyantar da ita, kuma ya sanar da ita kuma ya kyautata Sanar da ita, sannan ya Yantata sannan kuma ya Aureta, to yana da lada biyu.
5- "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"
6- Kun ganni na bakwai a cikin Bakwai Bakwai. Ba mu da wani bawa sai wanda ya mari karaminmu, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da 'yantar da ita