Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu

Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi waɗanda suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallah a lokacin addu'a ko waninta, sannan tsawatarwarsa ta yi tsanani da narkonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wanda ya aikata haka da cewa shi yana jin tsoro akan idanuwansu kada a fauce musu su a karɓesu da gaggawa ta inda basa ji sai kawai ga shi sun rasa n'imar gani.

فوائد الحديث

Kyakkyawan tsarin Da'awar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da bayanin gaskiya; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bayyana wanda ya saɓa ba; domin abin nufi shi ne bayanin gaskiya alhali kuwa ta tabbata; domin kuma a cikinsa akwai suturtawa ga mai saɓawa kuma ya fi sa a karɓa.

Hani mai ƙarfi, da narko mai tsanani akan wanda ya ɗaga ganinsa zuwa sama a cikin sallah.

Ya faɗa a cikin Aunil Ma'abud: Illa a cikin hakan cewa shi idan ya ɗaga ganinsa zuwa sama to ya fita daga saitin alƙibla kuma ya bijire mata dama siffar sallar.

Ɗaga ido zuwa sama yana kore Khushu'i a cikin sallah.

Girman sha'anin sallah, kuma yana wajaba akan mai sallah ya kasance a cikinta akan cikar ladabi tare da Allah - Mai girma da ɗaukaka -.

التصنيفات

Kusakuren Masu Sallah