إعدادات العرض
Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki
Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทยالشرح
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.فوائد الحديث
Haƙuri akan bala'i a duniya yana gadar da aljanna.
Nawawi ya ce: A cikin sa akwai dalili akan cewa farfaɗiya ana bada lada a kanta mafi cikar lada.
Kamewa da kunyar matan sahabbai, da kuma kwaɗayinsu akan suturta - Allah Ya yarda da su -, wannan matar ta kasance mafi yawan abinda take jin tsoro shi ne wani abu ya yaye daga jikinta.
Ibnu Hajar ya ce: Lallai yin riƙo da tsanani shi yafi daga yin riƙo da rangwami ga wanda ya san cewa akan kansa zai iya, kuma ba zai yi rauni ba saboda lazimtar tsanani.
Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa cewa maganin cututtuka gaba ɗayansu shi ne addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah ya fi tasiri kuma ya fi amfani daga magani da ƙwayoyi, kuma cewa tasirin hakan da kuma tasirin jiki daga gare shi ya fi girma daga tasirin magungunan jiki, sai dai kaɗai yana tasiri ne da al'amura biyu:
Na farkonsu ta ɓangaren wanda illar ta sama shi ne gaskiyar nufi, ɗayan kuma ta ɓangaren mai yin maganin, shi ne ƙarfin niyya da kuma ƙarfin zuciyarsa da tsoron Allah da kuma dogara, Allah ne Mafi sani.
Ibnu Hajar ya ce; A cikinsa akwai dalili akan halaccin barin yin magani.