Magani da bada Magani da Ruqya ta Shari’a

Magani da bada Magani da Ruqya ta Shari’a

3- "Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa,@ na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".