:

Daga Usman ɗan Abul Aas al-Saƙafi - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya kai kukan wani ciwo da yake jinsa a cikin jikinsa wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tunda ya musulunta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.

فوائد الحديث

An so mutum ya yi wa kansa tawaida kamar ydda ya zo a cikin hadisin.

Kai kuka - ba tare da kurari ba ko bijirewa - ba ya kore dogaro (ga Allah) da kuma haƙuri.

Addu'a tana daga jumlar aikata sabubba, saboda haka yana kamata a takaitu da lafazzukanta da kuma adadinta.

Wannan addu'ar tana kasancewa ne ga dukkan wani raɗaɗi na gaɓa.

Ɗora hannu akan wurin raɗaɗi a lokacin yin tawaida da wannan addu'ar.

التصنيفات

Ruqiyya ta Shari'a