Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne

Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana wasu abubuwa (waɗanda) aikatasu yana daga shirka; daga cikinsu akwai: Na ɗaya: Tawaida: Zancen da 'yan Jahiliyya suke neman waraka da shi wanda ya haɗo shirka. Na biyu: Layu na tsarkiya da makamancinta: Waɗanda ake ratayawa yara da dabbobi da wasunsu dan tunkuɗe kambun baka. Na uku: Tiwala: Wacce akeyi don jawo soyayyar ɗaya daga cikin ma'aurata zuwa ɗayan. Waɗannan al'amuran suna daga shirka; domin suna daga cikin riƙar abu a matsayin sababi, kuma shi ba sababi ne na shari'a ba wanda ya tabbata da dalili, ba kuma sababi ne na zahiri ba da ya tabbata da gwadawa. Amma sabubba na shari'a kamar karanta Al-ƙur'ani, ko na zahiri kamar magunguna da suka tabbata ta hanyar gwadawa, to, su sun halatta tare da ƙudire cewa su sabubba ne, kuma amfani da cuta suna hannun Allah ne.

فوائد الحديث

Kiyaye tauhidi da aƙida daga abin da yake ɓata su.

Haramta yin amfani tawaida ta shirka da layu da tiwala.

Ƙudirewar mutum a waɗannan abubuwa ukun cewa su sabubba ne: Shi ne shirka ƙarama; domin ya sanya abin da ba sababi ba ne a matsayin sababi, amma idan ya ƙudire cewa suna amfanarwa kuma suna cutarwa a kan kansu, to, shi shirka ne babba.

Gargaɗi a kan aikata sabubba na shirka da kuma ababen haramtawa.

Haramta (nau'o'in) tawaida kuma suna daga shirka, sai dai abin da aka shara'anta daga cikinsu.

Ya kamata a rataya zuciya ga Allah Shi kaɗai, cuta da amfani daga gareshi ne Shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkuɗe sharri sai Allah - Maɗaukakin sarki -.

Tawaida da ta halatta ita ce wacce ta tattaro sharuɗɗa uku; 1- Ya ƙudire cewa su sababi ne ba sa amfanarwa sai da izinin Allah. 2- Ta kasance da Al-ƙur'ani da kuma sunayen Allah da siffofinSa da addu'o'in Annabi da wasu ababen shara'antawa. 3- Ta zama da yare abin fahimta, kuma kada ta ƙunshi ɗalasimai (saƙandamai) da sha'awazah (surkulle).

التصنيفات

Ruqiyya ta Shari'a