«‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce*, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».

«‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce*, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».

Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa: «‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan kyautatawa muminai sashinsu ga sashi ko da da addu'a ne.

Addu'a a ɓoye tana nuni a bayyane akan gaskiyar imani da kuma 'yan uwantaka.

Ƙayyade addu'a da cewa a ɓoye; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a ikhlasi (wato yi domin Allah) da kuma halartowar zuciya.

Daga cikin sabubban amsa addu'a akwai musulmi ya yi wa ɗan'uwansa musulmi addu'a a ɓoye.

Nawawi ya ce; Falalar addu'a ga ɗan'uwansa musulmi a ɓoye, da a ce zai yi wa jama'ar musulmai addu'a to wannan falalar zata tabbata, da kuma a ce zai yi addu'a ga jumlar musulmai to zance mabayyani shi ne samuwar (falalar), wani daga cikin magabata na gari ya kasance idan yana so ya yi wa kansa addu'a sai ya yi wa ɗan'uwansa addu'a da wannan addu'ar; domin cewa ita za'a amsata, kuma zai samu kwatankwacinta.

Bayanin wasu daga cikin ayyukan Mala'iku, kuma cewa daga cikinsu akwai wanda Allah Ya wakilta shi ga wannan aikin.

التصنيفات

Imani da mala’iku, Falalar Addu'a