An zo wa Annabi Mai tsira da aminci su tabbata a gare shi da wani yaro, sai ya yi fitsari a kan tufafin Annabi, sai ya sa aka kawo masa ruwa ya yayyafa masa.

An zo wa Annabi Mai tsira da aminci su tabbata a gare shi da wani yaro, sai ya yi fitsari a kan tufafin Annabi, sai ya sa aka kawo masa ruwa ya yayyafa masa.

Daga Ummu Kais y'ar Mihsanin Al'asadiyya -Allah ya yarda da ita-" Ita ce ta zo wajen Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi da wani danta karami da bai fara cin abinci ba, sai Annabi ya zaunar da shi a dakinsa, sai ya yi fitsari a kan tufar Annabi, sai ya sa aka kawo ruwa ya yayyafa a kan tufafin, bai wanke ba" Daga A'isha Uwar muminai Allah ya yarda da ita- "An zo wa Annabi Mai tsira da aminci su tabbata a gare shi da wani yaro, sai ya yi fitsari a kan tufafin Annabi, sai ya sa aka kawo masa ruwa ya yayyafa masa" A wata ruwayar (sai ya bibiye shi da ruwa, bai wanke shi ba)

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Sahabbai Allah ya yarda da su sun kasance sukan zo wa Annabi tsira da amainci su tabbata gareshi da 'y'a'yansu don neman albarkasa da albarkar addu'arsa, Manzo tsira da amincin Allah saboda taushin halinsa da saukin kansa yakan taresu da murmushi da sakin fuska,sai Ummu Kais tazo da wani danta karami, mai shan nono. bai fara cin abinci ba, saboda tausayinsa sai ya zaunar da shi a dakinsa mai girma, sai yaron yayi fitsari a kan tufauin Annabi tsira da amaincin Allah, sai Annabi yasa aka kawo ruwa ya yayyafa wa tufafin amma bai wankeshi ba

التصنيفات

Gusar da Najasa