إعدادات العرض
1- Idan kuka je yin bayan gida, to kada ku kuskura ku Fuskanci Al'kibla da Bayan gida ko Bawali , kuma kada ku juya mata baya, sai dai ku fuskanci Gabas ko kuma Yamma
2- Idan Kare yasha a Kwaryar Dayanku ya wanketa sau Bakwai
3- Na kasance mutum mai yawan yin mazi, sai naji kunyar tambayar Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi saboda matsayin y'arsa a waje na, sai na uamrci Mikdad Dan Aswad, ya tambaye shi, sai Annabi yace: Ya wanke Azzakarinsa, ya yi alwalla
4- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, kuma ni da wani yaro muna dauke da na'urar ruwa da akuya, kuma zai yi tanadi da ruwa
5- Wani balaraben kauye ya zo ya yi fitsari a wani bangare na masallaci, sai mutane suka kyare shi, sai Annabi y hana su tsira da aminci su tabbata a gare shi, bayan ya gama fitsarin sai Annabi tsira da amaincin Allah ya yi umarni da a zo da cikakken guga na ruwa, sai aka kwara akai.
6- Na kasance cikin janaba sai na kyamaci in zauna a wajenka alhalin ba ni da tsarki, sai ya ce: subahanallah, ai mumini baya kasancewa najasa
7- An zo wa Annabi Mai tsira da aminci su tabbata a gare shi da wani yaro, sai ya yi fitsari a kan tufafin Annabi, sai ya sa aka kawo masa ruwa ya yayyafa masa.
8- "Ku rabu da shi ku zuba Bokitin Ruwa, ko Gugan Ruwa, Saboda an turo ku ne Masu saukakakawa ba'a turoku masu tsanantawa ba"
9- Ana Wanke futsarin Baiwa, kuma a yayyafa Ruwa a Futsarin yaro
10- Tana kankare shi, sannan ta wanke shi da Ruwa, ta kuma yayyafa masa Ruwa, kuma tayi sallah da shi
11- Idan ya taka Najasa da Takalmansa, to tsakakesu shi ne Qasa