Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya kasance da wani mai yin hidima sa'ansa a shekaru suna bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya fita dan biyan buƙatarsa, suna ɗaukar masa sanda mai kai irin kan goron mashi dan ya sanyata kariya da zai rataya wani abu a kanta yana mai suturtawa ko kuma sutura ga sallarsa, kuma suna ɗaukar masa ƙaramar ƙwarya na fata wacce take a cike da ruwa, idan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gama biyan buƙatarsa sai ɗaya daga cikinsu ya ba shi ƙwaryar, sai ya yi tsarki da ruwa.

فوائد الحديث

Musulmi ya yi tanadin ruwan tsarki a lokacin biyan buƙata; dan kada ya buƙatar da shi zuwa tashi sai ya ɓata jikinsa.

Kiyaye al'aura a lokacin biyan buƙata dan kada wani ya ganta; domin kallon al'aura haramun ne, ya kasance yana kafa sanda a ƙasa kuma yana shinfiɗa tufa mai suturtawa a kanta.

Koyar da yara ladubban Musulunci da kuma tarbiyantar da su akanta; dan su gaje su (su saba da su).

التصنيفات

Falalar Sahabbai -Allah yayarda da su-, Hadimansa SAW, Gusar da Najasa, Ladaban biyan bukata, Koyarwarsa SAW a wajen tsarki