"Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma"* Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".

"Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma"* Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi nufin biyan buƙatarsa na fitsarine ko bayan gida ya fuskanci alƙibla wajen Ka'aba, kuma kada ya juya mata baya, ya sanyata a bayansa; kai ya wajaba akansa ne ya juya ɓangaren gabas ko yamma idan alƙiblarsa kamar alƙiblar mutanen Madina ce. Sannan Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su lokacin da suka je Sham sun samu banɗakunan da aka tanada dan biyan buƙata a cikinsu an gina su suna fuskantar Ka'aba, sun kasance suna juyawa alƙibla baya da jikkunasu, tare da hakan suna neman gafarar Allah.

فوائد الحديث

Hikima a hakan shi ne girmama Ka'aba maɗaukakiya da ganin alfarmarta.

Neman gafara bayan fitowa daga gurin biyan buƙata.

Kyakkyawan koyarwar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi lokacin da ya ambaci wanda aka hana sai ya shiryar zuwa ga wanda ya halatta.

التصنيفات

Gusar da Najasa, Ladaban biyan bukata