Na kasance cikin janaba sai na kyamaci in zauna a wajenka alhalin ba ni da tsarki, sai ya ce: subahanallah, ai mumini baya kasancewa najasa

Na kasance cikin janaba sai na kyamaci in zauna a wajenka alhalin ba ni da tsarki, sai ya ce: subahanallah, ai mumini baya kasancewa najasa

An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi - marfu'i: "lallai Annabi tsira da amincin Allah ya hadu da shi a wata hanya ta Madina alhali yana da janaba. sai yace: sai na sulale daga wajen shi, sai na tafi na yi wanka sannan na dawo, sai Annabi ya ce: ina kaje ya Aba Huraira? sai ya ce: Na kasance cikin janaba sai na kyamaci in zauna awajenka alhalin ba ni da tsarki, sai yace: subhanallah ai mumini baya kasancewa najasa

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abu Huraira ya hadu da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wata hanya ta Madina, a lokacin kuma Abu HUraira yana da janaba a jikinsa, sa yaki ya zauna a wajen Annabi yana a wannan halin, sai ya sulale a boye daga wajen Annabi ya je ya yi wanka sannan ya dawo. sai Annabi ya tambaye shi ina ya je, sai Abu Huraira ya baiwa Annab labarin halin da yake ciki, cewar bazai iya zama a wajen Manzo ba alhali da janaba a jikinsa, sai Annabi ya yi mamakin Abu Huraira da ya tsammaci kaasantuwan mai janaba naja sa ne, har ya tafi ya yi wanka ya kuma zo ya bashi labari, tare da cewa mumini ba zai taba zama najasa ba

التصنيفات

Gusar da Najasa, Wanka