Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai

Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da wanke kwarya sau bakwai idan kare ya shigar da harshensa a cikinta, na farko daga cikinsu a haɗa da turbaya sai ruwa ya biyo bayanta, sai cikakkiyar tsafta ta tabbata daga najasarsa da kuma cutarsa.

فوائد الحديث

Yawun kare najasa ne najasa mai kauri.

Lallagin kare a cikin kwarya yana maida ita mai najasa, kuma yana najasantar da ruwan dake cikinta.

Tsarkakewa da turbaya da maimaitawa sau bakwai ya kebanci tsarkakewa ne daga lallaginsa banda fitsarinsa da bayan gidansa, da ragowar abinda kare ya bata shi .

Yadda wanke kwarya da turbaya: A sanya ruwa a cikin kwarya sai a zuba turbaya (kasa) a ciki, sannan a wanke kwarya da wannan cuɗaɗɗen.

Zahirin Hadisin mai gamewa ne a dukkanin karnuka, har karnukan da shari’a ta bada iznin a dauke su, misalin karnukan farauta da na gadi da na kiwo.

Sabulu da makilin ba sa tsayawa a matsayin turbaya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nassanta turbaya ne.

التصنيفات

Gusar da Najasa, Kwanuka