إعدادات العرض
Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a)
Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a)
Daga Zirr Dan Hubaish ya ce: Na zo wurin Sufwan bn Assal al-Muradi - Allah Ya yarda da shi - ina tambayarsa game da shafa akan huffi, sai ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? Sai na ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai Mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi, dan yarda da abinda yake nema, sai na ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi da bawali ya sosu a cikin zuciyata, kai kuma mutum ne daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na zo ina tambayarka: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a cikin hakan? Ya ce: Eh, Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a), sai na ce: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a sha'anin soyayya? ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a halin tafiya lokacin muna wurinsa sai wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa gwargwadan muryarsa: «Haum» kuma mukace da shi: Kaicanka ka ƙanƙanta muryarka, lallai kai kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:, alhali an hanaka wannan, sai ya ce: Wallahi bazan ƙanƙar da muryata ba, balaraben ƙauyen ya ce: Mutum yana son mutane amma bai risku da su ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: ya ce: «Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama» bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofa a ɓangaren yamma, tafiyar faɗinta, ko mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog Kurdî Русский دری Português Македонски Tiếng Việt Magyar ქართულიالشرح
Zir bn Hubaish ya zo wurin Safwan bn Assal - Allah Ya yarda da shi -, yana tambayarsa game da shafa akan huffi, sai Safwan ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? sai ya ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi; dan yarda da girmamawa ga abin da mai neman ilimi yake aikatawa, sai Zir ya ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi ko fitsari ya yi kai kawo a cikin zuciyata, alhali kai kana daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ya sa nazo ina tambayarka shin ka ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wani abu a kan haka? Safwan ya ce: Eh, ya kasance yana umartarmu idan mun kasance matafiya kada mu cire huffunanmu tsawon kwana uku da dararensu saboda hadasi ƙarami, kamar gayaɗi da fitsari da bacci, sai dai saboda janaba kawai, to ya wajaba a cire, sai na ce: Shin ka ji shi ya faɗi wani abu game da so? Ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wata tafiya mun kasance muna wurinsa sai ga wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da babbar murya kusa da muryarsa: Zo, sai mukace masa: Kaicanka ka ƙanƙar da muyarka, kaifa kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali an hanaka ɗaga murya a wurinsa. Saboda kakkausan halinsa sai ya ce: Wallahi ba zan ƙanƙar da muryar ba, sai balaraben ƙauyen ya ce: Ya Manzon Allah, mutum yana son mutane nagari amma bai yi irin aikinsu ba? Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama, Zir ya ce: Safwan bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofar tuba a ɓangaren Sham, Allah Ya halicceta ranar halittar sammai da ƙasa, mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in, kuma ba za'a kulleta ba har sai rana ta ɓullo ta yammacinta.فوائد الحديث
Bayanin kwaɗayin Tabi'ai akan neman ilimi daga sahabbai - Allah Ya yarda da su -.
Halaccin shafa akan huffi, da kuma adadin kwanakinsa, yini uku da dararensu ga matafiyi, mazaunin gida kuma yini ɗaya da darensa.
Shafa akan Huffi tana kasancewa ne a ƙaramin hadasi kadai.
Halaccin mai tambaya ya nemi malami ya faɗa masa dalilinsa, shin nassi ne ko kuma kafa hujja ne da kuma ijtihadinsa, kuma ya wajaba akan malami kada ya ji damuwa akan hakan.
Ladabi tare da malamai da mutanen kirki, da ƙanƙar da murya a majalisan ilimi.
Sanar da jahili kyawawan ladabi da ƙa'idodjin Tarbiya.
Kwaɗaitarwa akan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a haƙurinsa, da kyawawan ɗabi'unsa, da yadda yake magana da mutane gwargwadon ilimunsu da kuma hankulansu.
Al-Mubarakafuri ya ce: Kaɗai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya ɗaga muryarsa ne ta hanyar tausaya masa dan kada aikinsa ya ɓaci saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Kada ku ɗaga muryarku sama da muryar Annabi}; sai ya yi masa uzuri saboda jahilcinsa, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga muryarsa ne har ta zama kwatankwacin muryarsa (shi mutumin) ko sama da ita dan yawan tausayinsa.
Kwaɗaitarwa akan zama da salihai da kusantowa zuwa garesu da kuma son su.
Nawawi ya ce: Kasancewarsa tare da su ba ya hukunta matsayinsa da sakamakonsa ya zama kwatankwacin nasu ta kowanne ɓangare.
Buɗe ƙofar fata da kwaɗayi da albishir da tsira, da tausasawa a cikin wa'azi.
Yalwar rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da buɗewarsa ƙofar tuba.
Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba da yi wa zuciya hisabi da komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
التصنيفات
Shafa a kan Huffi da waninsa