Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga

Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadakar da wanda zai yi hamma cewa buɗe bakinsa saboda kasala ce ko cika ko wanin haka; cewa ya ɗora hannunsa akan bakinsa sai ya rufeshi da shi; hakan domin Shaiɗan yana shiga cikinsa idan ya barshi a buɗe, to ɗora hannu yana zama mai hana shigarsa.

فوائد الحديث

Idan mutum yana son yin hamma to ya wajaba a kansa ya rufe (bakinsa) daidai iko, cewa ya riƙe bakinsa, sai ya barshi a rufe ta inda ba zai buɗe ba, idan ba zai iya barin bakinsa a rufe ba to ya ɗora hannunsa akan bakinsa, sai ya rufe bakinsa da hannunsa.

Lazimtar ladubban Musulunci a dukkan halaye; domin cewa sune alamomi na cika da kuma ɗabi'u.

Kiyayewa daga dukkan mashigar Shaiɗan ga mutum.

التصنيفات

Ladaban Atishawa da Hamma