إعدادات العرض
Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi
Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Tiếng Việt Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta wanda ya karanta Alƙur'ani kuma ya saba da karanta shi - daidai ne yana dubawa daga Mushafi ne ko da ka yake yi - da ma'abocin dabaibayayyun raƙuma da igiyar da ake ɗaure gwiwowin raƙuma da su, idan ya kula sai ya ci gaba da riƙesu, idan kuma ya saki ɗaurinsu sai su tafi su suɓuce, idan ma'abocin Alƙur'ani ya tsaya sai ya karanta shi zai tuna shi, idan kuma bai tsayu da shi ba to zai manta shi; lazimta ba zata gushe tana samammiya ba sai hadda itama ta zama tana nan.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa akan lazimtara Alƙur'ani da kuma karanta shi, da kiyayewa daga bijirar da shi ga mantuwa.
Dawwama akan karatun Alƙur'ani harshensa zai horu da shi kuma karanta shi zai yi masa sauƙi, idan ya ƙaurace masa sai karatun ya yi masa nauyi kuma ya wahalar da shi.
Alƙali ya ce: Ma'anar "Ma'abocin Alƙur'ani" wato: Wanda ya saba da shi, al-Musahaba: Sabo da abu, daga haka ne: Wane abokin wane ne, da 'yan aljanna da kuma 'yan wuta.
Daga cikin hanyoyin Da'awah akwai buga misalai.
Ibnu Hajar ya ce: An keɓanci raƙuma da ambato; domin cewa sune mafi tsananin gujewa cikin dabbobin gida, kuma kama su bayan sun gudu akwai wahala.