Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta

Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa haƙiƙa ya rabauta wanda ya miƙa wuya ga Ubangijinsa sai aka shiryar da shi kuma aka datar da shi ga Musulunci, kuma aka azirta shi gwagwadan buƙatarsa daga halal ba tare da ƙari ko ragi ba, kuma Allah Ya sanya shi mai yarda da abinda Ya bashi.

فوائد الحديث

Kwanciyar hankalin mutum yana cikin cikar Addininsa da isuwar abin cinsa da kuma wadatuwarsa da abinda Allah Ya ba shi.

Kwaɗaitarwa a kan wadatuwa da abinda aka baka na duniya tare da Musulunci da kuma sunnah.

التصنيفات

Zargin Son Duniya