Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa

Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wata rana wani mutum yana tafiya sai ya wuce wani reshen bishiya a cikinsa akwai ƙayar da take cutar da musulmai, sai ya kawar da ita daga hanyar, sai Allah Ya yaba masa kuma Ya gafarta masa.

فوائد الحديث

Falalar gusar da cuta akan hanya, kuma hakan sababi ne na (samun) gafarar Allah.

Rashin wulaƙantar da ayyukan alheri koda sun kasance kaɗan ne.

Musulunci addini ne na tsafta da kare yanayi da aminci na gaba daya.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai