إعدادات العرض
Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi
Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi».
الترجمة
العربية Português دری Македонски Magyar Tiếng Việt ქართული বাংলা Kurdî ไทย অসমীয়া Nederlands ਪੰਜਾਬੀ Bahasa Indonesia Kiswahiliالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.فوائد الحديث
Girman ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Ibnu Hajar ya ce: A cikin Hadisin akwai cikar tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kyawawan ɗabi'unsa da karamcin zatinsa, inda ya fuskanci abin da ya afku daga gare shi da gyarawa da kuma girmamawa.
Nawawi ya ce: Idan an ce: Ta yaya zai yi mummunar addu'a akan wanda bai cancanci mummunar addu'a ba ? ko ya zage shi ko ya tsine masa da makamancin hakan? Amsa ita ce abin da malamai suka amsa da shi, a taƙaice ta fuska biyu:
Na farkonsu: Abin da ake nufi da wanda bai cancanci hakan ba a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -, haka a cikin baɗinin al'amari, sai dai cewa shi a zahiri ya cancanci hakan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanar da cancantarsa ga hakan da alamu na shari'a, kuma ya zama a baɗini al'amari bai cancanci hakan ba, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abin umarta ne da yin hukunci a zahiri, Allah ne Yake jiɓintar sirrika.
Na biyu: Cewa abin da ya faru na zaginsa da mummunar addu'arsa da makancinsa to ba abin nufi ba ne, kai shi yana daga abin da al'adar larabawa ta gudana da shi a cikin sadar da zancensu ba tare da niyya ba. Kamar faɗinsa: Damanka ya talauta, da ciwo ya sameka a fata da maƙogwaro, a cikin wannan hadisn: (Kada shekarunka su yi yawa), a cikin hadisin Mu'awiya: Kada Allah Ya ƙosar da cikinka, da makamancin haka, basa nufin wani abu daga haƙiƙanin addu'a, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ji tsoron kada amsa addu'ar ta dace da wani abu daga hakan, sai ya roƙi Ubangijinsa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya kwaɗaitar da ya sanya hakan ya zama rahama da kaffara da kusanci da tsarkakkewa da kuma lada, kaɗai hakan yana bayyana ne daga gare shi a lokaci kaɗan daga cikin zamaninsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mai alfasha ba, haka ba ya ɗorawa kansa yawan yin alfasha, kuma ba mai yawan tsinuwa ba ne, ba kuma mai ɗaukar fansa ne da kansa ba.
التصنيفات
Siffarsa ta Halayya