Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba

Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin dokin da aka tanada dan tsere mai sauri a cikin gudunsa zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai tiƙe ga ƙarshen abinda ya karkace daga ressanta ba.

فوائد الحديث

Bayanin yalwar aljanna, da girman bishiyoyinta.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta