إعدادات العرض
Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: …
Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Bata baccin dare! @Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Bata baccin dare! Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog ئۇيغۇرچە Kurdî Tiếng Việt Magyar ქართული සිංහල Kiswahili Română অসমীয়া ไทย Portuguêsالشرح
Haula'u Bnt Tuwait - Allah Ya yarda da ita - ta kasance a wurin uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo gurinta (Nana A'isha), sai (Haula'u) ta fita ta barta Sai Nana A'isha ta ce masa: Wannan matar bata baccin dare, kai tana raya shi da sallah. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai tsananin yi mata inkari: Bata baccin dare! ku shagalta da aiki na gari wanda zaku iya dawwama a kansa, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa akan baiwa bayinSa salihai masu biyayya lada da sakamako akan biyayyarsu da kuma kyawawan ayyukansu da kuma ayyukansu na gari har sai sun ƙosa sun bar aikin.فوائد الحديث
Yawaita ibada sama da yadda jiki zai iya, yana kaiwa zuwa ga ƙosawa da kuma yankewa sai zuciya ta daina yin aikin.
Daidaituwa da tsakatsaki a cikin yin ibada hakan yana sawa a ci gaba da ibadar da kuma tabbata a kanta.
Kanƙanin aiki da aka dawwama ana yi ya fi alheri akan aiki mai yawa mai sa a yanke aikin.
Nawawi ya ce: Ta hanyar dawwama da aiki kaɗan ɗa'a tana zarcewa da zikiri da muraƙaba da ikhlasi da kuma fuskanta ga Allah, saɓanin aiki mai yawa mai wahalarwa har aiki ɗan kaɗan ya ƙaru ta inda zai fi mai yawa wanda aka daina da lada mai yawa.
التصنيفات
Haqqin Xan Adam a Musulunci