Dauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba

Dauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba

Daga Aisha Allah ya yarda da ita tace: "Hindu 'yar Utbata - Matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai tace: Ya Manzon Allah, Abu Sufryan ya kasance mutum ne mai rowa, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai dai in na dauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba. Shin ba laifi akan yin hakan? Sai Manzo tsira da amincin Allah yace: Dauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Hidu 'yar Utbata ta tambayi Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa mijinta baya bata abin da zai ishe ta ita da 'ya'yanta shin ko zata iya dauk cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba? sai yayi mata fatawa da halarcin yin hakan amma kar ta wuce abin da zai ishe su.

التصنيفات

Ciyarwa