Shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai kuma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta kuma ku halarta shi ba? sai na ce:e. sai ya ce wannan shi ne ibadarsu.

Shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai kuma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta kuma ku halarta shi ba? sai na ce:e. sai ya ce wannan shi ne ibadarsu.

An samo daga Adi Dan Hatim -Allah ya yarda dashi- "cewa ya ji Annabi -tsira da amincin Allah yana karanta wannan ayar: Sun riki malamansu "yahudawa" da malamansu "nasarawa" abin yiwa bauta ba Allah ba haka nan Isa Dan Maryam. kuma ba'a umarce su ba sai da cewa su bautawa abin bauta shi kadai wanda ba abin bautawa da cancanta sai shi tsarki ya tabbatar masa game da abin da suke yi masa tarayya? sai na ce da shi: lallai mu ba bauta musu muke yi ba. sai ya ce: shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai ku ma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta ku ma ku halarta shi ba? sai nace: ey.Sai yace wannan ita ce bauta musu din."

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

yayin da wannan Sahabin mai girma yaji karatun Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-na wannan ayar wacce ta kunshi labarin yahudu da nasara:cewa sun mayar da malamansu da masu ibadar cikinsu abin bauta,suna shar'anta musu abinda yasabawa shari'ar Allah kuma suyi musu biyayya a kan haka,to sai ma'anar ayar ta rikitar,domin shi sahabin ya zaci cewa bauta ta takaita akan yin sujjada da makamantanta,sai Manzo -tsira da amincin Allah-ya bayyana masa cewa yana daga bautawa malamai yi musu biyayya a wajan haramta halal da kuma halarta haram,sabanin hukunci Allah madaukaki da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi

التصنيفات

Shirka