Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi*, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina…

Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi*, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».

Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».

فوائد الحديث

Tsananin kwaɗayin sahabbai akan alheri da neman ƙaruwar shi da kuma neman lada.

Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da lada a cikin takun dawowa daga sallah kamar yadda yake tabbata a tafiya.

Musulmi su yi wa junansu wasiyya da alheri da kuma nasiha da aikin alheri, wanda ya ga cewa ɗan'uwansa wata wahala tana riskarsa to ya gabatar masa da nasiha a gusar da ita.

Nisan gida daga masallaci ba uzuri ba ne a kan barin jam’i, muddin dai yana jin kiran sallah.

التصنيفات

Falalar musulunci da kyawawan koyarwarsa