إعدادات العرض
Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba
Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Tiếng Việt Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna ana kiranta: Kofar Rayyan, masu azimi zasu shigeta ranar alƙiyama, babu wanda zai shiga (aljanna) ta kofar sai su, za’a yi kira: Ina masu azimi, sai su miƙe su shiga, waninsu ba zai shiga ba, idan na ƙarshensu ya shiga sai akulleta, babu wani da zai shiga bayan nan.فوائد الحديث
Nawawi ya ce: A cikin hadisin akwai falalar azimi da kuma girman masu azimin.
Allah Ya ware wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna guda takwas ga masu azimi, idan suka shiga ta kofar sai akulleta.
Bayanin cewa aljanna tana da ƙofofi.
Sindi ya ce: Faɗinsa: (Ina masu azimi), wato masu yawaita yin azimi kamar mai adalci da azzalimi, ana faɗin haka ga wanda ya saba da hakan, ba ga wanda ya aikata sau ɗaya ba kawai.
(al-Rayyan) yana nufin wacce take ƙosarwa; domin cewa masu azimi suna jin ƙishirwa musammanma dai acikin kwanukan bazara masu tsawo masu zafi; sai a yi musu sakayya da ambatan wannan ƙofar da abinda yake keɓantarsu da shi da sunan ƙofar Arrayyan, kuma an ce Arrayyan wato Fa'alan mai yawan ƙoshi kishiyar ƙishirwa, an anbaceta da shi; domin cewa ita sakamakon masu azimi ce saboda ƙishirwarsu da kuma yunwarsu.
التصنيفات
Falalar Azumi