«Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».

«Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wata rayuwa ta haƙiƙa sai rayuwar lahira, a cikin yardar Allah da rahamarSa da kuma aljannarSa; domin rayuwar duniya mai gushewa ce, rayuwar lahira kuwa ita ce dawwamammiya mai wanzuwa, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar gafara da girmamawa da gyaruwa ga mutanen Madina waɗanda suka kawo ɗauki ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Muhajirun, suka taimakesu, suka raba musu dukiyoyinsu, kuma (ya yi addu'a) ga Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da kuma yarda.

فوائد الحديث

Gudun duniyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duniya da kuma fuskantowarsa ga lahira.

Gargaɗawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa a jin daɗin rayuwar duniya mai gushewa.

Bayanin darajar Muhajirai da Ansar, inda suka rabauta da addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - garesu da gafara.

Kada bawa ya yi farin ciki da abinda yake samu na duniya, ita mai saurin gushewa ce tare da abinda ke cikinta na gurɓacewa, kaɗai gidan tabbata shi ne gidan lahira.

التصنيفات

Zargin Son Duniya