Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi

Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bawa Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - labarin cewa wanda ya yi imani da Allah kuma ya yarda da Shi a matsayin Ubangiji abin bauta kuma shugaba kuma mai umarni, kuma da Musulunci a matsayin Addini dan jawuwa da miƙa wuya da dukkanin umarce-umarcensa da hane-hanensa, da kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da dukkan abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi; to aljanna ta tabbata gareshi, sai Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki ga (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaita mini ita ya Manzon Allah, sai ya aikata, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kuma ina da wata dabi'ar daban wacce Allah Yake daukaka darajar bawa da ita sau dari a cikin aljanna, tsakanin kowace darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa ne, Abu Sa'ida ya ce: Waccece ya Manzon Allah? ya ce: Jihadi a tafarkin Allah, jihhadi a tafarkin Allah.

فوائد الحديث

Daga abubuwan da suke tabbatar da shiga aljanna yarda da Allah da kuma Musulunci a matsayin Addini da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi.

Girmama al'amarin jihadi a tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Ɗaukaka matsayin yaƙi a cikin aljanna.

Akwai wasu darajoji a cikin aljanna ba sa ƙirguwa, da matsayin da ba za su ƙirgu ba, kuma mayaƙa suna da darajoji ɗari daga cikinsu.

Soyayyar sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sanin alheri, da ƙofofinsa da kuma sabubbansa.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta, Falalar Jahadi