إعدادات العرض
Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu
Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Kiswahili Português සිංහල Nederlands Tiếng Việt অসমীয়া ગુજરાતી አማርኛ پښتوالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba a ranar lahira wanda yake da takalma biyu da igiyoyi biyu ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa saboda zafinsu, kamar yadda tukunyar tagulla take tafarfasa, kuma ba ya ganin wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi ne mafi sauƙin azabarsu, hakan dan azabar jiki da ta rai su haɗu a kansa.فوائد الحديث
Tsoratar da masu saɓo da kafirai daga tsoron wannan azabar a cikin wuta; dan su nisanci abinda zai kai zuwa gareta.
Banbacin matsayin masu shiga wuta gwargwadan mummunar ayyukansu.
Tsananin azabar wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kuɓutar da mu daga gareta.
التصنيفات
Sifar Al-janna da Wuta