Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

Daga Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - yana ambatawa mutane abinda suke a cikinsa na ni'ima, kuma su basu gushe ba suna yadda suke so a cikin abin cin da abin sha, sannan ya bada labarin halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi bai kasance yana samun dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi saboda yunwa ba.

فوائد الحديث

Bayanin halin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa na gudun duniya.

Kwaɗaitarwa akan gudun duniya da kuma ƙarantuwa daga gareta da kuma koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Tunatar da mutane ni'imomin da suke a cikinsu da kuma kwaɗaitarwa akan godewa Allah a kansu.

التصنيفات

Zargin Son Duniya