Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka

Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.

فوائد الحديث

Yawan ƙofofin ciyarwa a tafarkin Allah.

Gabatar da abin da ya fi a cikin babin ciyarwa a lokacin cinkoso, yana daga hakan ciyarwa ga iyali a lokacin da ciyarwa ga gabaɗayan ba zai yi wu ba.

Nawawi ya faɗa a Sharhin Muslim: Kwaɗaitarwa akan ciyarwa ga iyalai, da kuma bayanin girman lada a cikinta; domin daga cikinsu akwai wanda ciyarwarsa take wajaba ta hanyar kusanci, daga cikinsu akwai wanda take zama mustahabbi kuma tana zama sadaka da sada zumunci, kuma daga cikinsu akwai wadda take zama wajiba ta hanyar mallakar aure ko mallakar dama (bayi), wannan dukkansa mai falala ne kuma abin kwaɗaitarwa ne a kansa, kuma shi ya fi sadakar nafila.

Sindi ya ce: Faɗinsa: (Dinaren da yake ciyar da shi ga iyalansa), wato: Idan ya yi hakan don Allah kuma ya yi nufin haƙƙin iyalai misali.

Abu Kilaba ya ce; Wane mutum ne mafi girman lada daga mutumin da yake ciyarwa ga iyalai ƙanana da zai karesu ko Allah Ya anfanar da su da shi kuma ya wadata su?!

التصنيفات

Ciyarwa, Sadakar Taxawwu'i