إعدادات العرض
Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi
Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi
Daga Salmanul Farisi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi: Dattijo mazinaci, da talaka mai girman kai, da mutumin da ya sanya Allah wata haja, ba ya sayarwa kuma ba ya siya sai da rantsuwarsa».
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Русский Tiếng Việt Magyar ქართული Kiswahili සිංහල Română অসমীয়া ไทย Português मराठी دری አማርኛ ភាសាខ្មែរالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu nau’uka uku na mutane, waɗanda suka cancanci uƙubar Allah a ranar alƙiyama da uƙuba uku idan basu tuba ba, ko a gafarta musu uƙubar ba: Ta farko: Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama saboda tsananin fushinSa, kai zai bijire musu, ko Ya yi musu maganar da ba zata faranta musu rai ba kuma yana nuni akan fushinSa akansu. Ta biyu: Ba zai tsarkakesu ba kuma ba zai yabesu ba kuma ba zai tsarkakesu daga zunubai ba. Ta uku: Azaba mai sa ciwo mai tsanani a lahira ta tabbata agare su. Waɗannan sinfofin na mutane sune: Sinfi na farko: Babban mutum kuma yake afkawa a cikin alfashar zina. Na biyu: Talaka mara dukiya, amma tare da haka yake yi wa mutane girman kai. Na uku: Wanda yake yawan rantsuwa da Allah a cikin saye da siyarwa, sai ya wulaƙanta sunan Allah, kuma ya sanya shi tsani dan samun dukiya.فوائد الحديث
Alƙali Iyad ya faɗa a cikin sababin wannan uƙubar mai tsanani: Cewa kowane ɗaya daga cikinsu ya lazimci saɓon da aka ambata tare da nisantarta daga gare shi, da kuma rashin larurarsa zuwa gare shi, da raunin abinda yake jawosu gare shi; duk da ba'a yi wa wani uzuri akan zunubi, saidai yayin da ya kasance babu wata larura mai takurawa zuwa ga waɗannan laifukan, kuma babu wasu masu sawa a yi laifukan na al'ada, sai aikatasu ya yi kama da tsaurin kai, da kuma wulaƙantar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -, da kuma nufatar saɓa maSa badan wata buƙatar waninsu ba.
Zina da ƙarya da girman kai suna daga cikin manyan zunubai.
Girman kai: Shi ne kin karbar gaskiya, da kuma wulaƙanta mutane.
Gargaɗarwa akan yawan yin rantsuwa a cikin saye da sayarwa, da kuma kwaɗaitarwa akan girmama rantsuwa, da girmama sunayen Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: (Kada ku mayar da Allah Ya zama kariya ga rantse-rantsenku) [al-Baƙara: 224].
التصنيفات
Zargin Savo